Isa ga babban shafi

MDD ta zargi Rasha, Ukraine da kisan fursunonin yaki

Majalisar dinkin duniya ta zargi sojojin kasashen Ukraine da Rasha da kisan fursunonin yakin juna a ci gaba da yakin da kasashen biyu ke gwabzawa.

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.
Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres. © Hadi Mizban / AP
Talla

Bayanin na majalisar dinkin duniya na zuwa ne, jim kadan bayan da Ukraine ta zargi Rasha da kisan wani ma’aikacin kasar ta Ukraine, wanda ke daukar Hoton bidiyon kansa yana yi wa Ukraine fatan alkahiri.

A karin bayanin da ta yi, Babbar jami’ar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya a Ukraine Matilda Bogner ta ce a baya-bayan nan sun tattara bayanan yadda sojojin juna ke kisan fursunonin da suke kamawa ba ji ba gani.

Ta ce karamin misali shine yadda a makon da ya gabata sojojin Ukraine suka kashe Fursunonin yaki 25 da suka kama daga Rasha, kuma hakan shine ya faru da Fursunonin yaki da Russia ta kama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.