Yawan makaman nukiliya ya karu a shekarar 2022 - Rahoto
Wani sabon rahoto ya ce yawan makaman nukiliya sun karu a shekarar 2022, lamarin da aka yi ittifakin ya wanzu ne da sa hannun China da Rasha, inda ya kara da cewa tun da aka fara yaki a Ukraine, barazanar nukiliya ta ta’azzara.
Wallafawa ranar:
Rahoton da wata kungiya mai zaman kanta, ta kasar Norway, wato Norwegian People’s Aid ta wallafa ya ce akwai makaman nukiliyar da za a iya amfanin da su, wadanda suka kai dubu 9 da 576 a shekarar 2023, abin da ke nufin sun karu daga dubu 9 da 440 da ake da su a shekarar 2022.
Rahoton ya ce wadannan makamai suna da karfin yin barna da ta kai sama da ta bama-bamai dubu 135 da aka jefa a Hiroshima a lokacin yakin duniya na 2.
An wallafa wadannan alkalumman ne a daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da nanataa barazanar amfani da makaman nukiliya, idan har kasahen yammacin Turaai suka ci gaba da bai wa Ukraine gudummawar makamai don ta kare kanta daga mamayar da ake mata.
A ranar Asabar, shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da cewa ya cimma yarjejeniya da Belarus don jibge kawarya-kwaryar makaman nukiliya a yankinta.
An dangata Karin makaman nukiliya 139 a duniya a shekarar da ta gabata da kasashen Rasha, wadda ta fi yawan makaman a duniya, inda ya kai har dubu 5 da 889 sai kuma China, India, Koriya ta Arewa da Pakistan.
Kasashen da ke da karfin nukiliya a hukumance a duniya kuwa sune, Amurka, Rasha, Birtaniya, Faransa, China, India, Paksitan, a yayin da Isra’ila tana da su amma ba a hukumance ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu