Biden ya bukaci Rasha ta saki dan jaridar Amurka
Shugaba Joe Biden na Amurka ya bukaci Rasha ta saki dan jaridar Wall Street Journal da ta kame a jiya alhamis bisa zarginsa da aikata liken asiri, kuma ake tsare da shi a gidan yarin Moscow.
Wallafawa ranar:
Kiran na shugaba Biden na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotu a birnin Moscow ta umarci ci gaba da tsare dan jaridar Amurkan Evan Gershkovich har na tsawon wata guda gabanin fara yi masa shari’a bisa zargin sa da aikata leken asiri a Rashan.
Tun gabanin kiran na Biden, jaridar Wall Street Journal da Gershkovich ke yi wa aiki ta bukaci lallai Rasha ta gaggauta sakin dan jaridar tare da neman Amurka ta kori jakadan Moscow a Washington da dukkanin ‘yan jaridar kasar saboda abin da mahukunta suka aikata.
Dan jaridar na Amurka ya musanta a gaban kotu cewa babu kanshin gaskiya a zargin da ake masa na leken asirin, amma hukumomin Rasha sun yi mursisi .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu