Isa ga babban shafi

Indiya ta zarta China da yawan jama'a a duniya

Indiya za ta wuce China a matsayin kasa mafi yawan jama'a a duniya a karshen watan Yuni, alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa, hakan zai haifar da babban kalubale ga kasar da ke kokarin samar da ababen more rayuwa daidai lokaccin da take fama da rashin isassun ayyukan yi ga miliyoyin matasa.

Yadda mutane ke sayen abinci a bakin hanya cikin wata kasuwa da ke New Delhi na kasar Indiya, an dauki hoton a watan Nuwamba, 2022.
Yadda mutane ke sayen abinci a bakin hanya cikin wata kasuwa da ke New Delhi na kasar Indiya, an dauki hoton a watan Nuwamba, 2022. AP - Altaf Qadri
Talla

Alkaluman sun nuna cewa yawan al'ummar Indiya ya kai sama da biliyan 1.400 inda yah aura adadin yawan al’ummar kasar China da miliyan uku, wanda ke da adadin sama da mutum biliyan daya, in ji rahoton hukumar kula da yawan jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya.

A baya dai ana kallon China a matsayin kasa mafi yawan al'umma a duniya tun bayan faduwar daular Rum amma a bara yawan al'ummarta ya ragu a karon farko tun 1960, yayin da na Indiya ke ci gaba da karuwa.

Kasar da ta kasance mafi girma a Kudancin Asiya ta bazu daga yankin Himalaya zuwa bakin teku na Kerala, ana amfani da harsunan har guda 22, kuma kusan rabin mazauna yankin basu haura shekaru 25 da haihuwa.

Kasar na fuskantar manyan kalubale wajen samar da wutar lantarki da abinci da gidaje ga al’ummarta, inda da yawa daga cikin manya-manyan garuruwan kasar sun jima suna fama da matsalar karancin ruwa, gurbacewar iska da ruwa, da kuma matsuguni.

A cewar cibiyar bincike ta Pew, adadin mutanen Indiya ya karu da fiye da biliyan daya tun daga 1950, shekarar da Majalisar Dinkin Duniya ta fara tattara bayanan yawan jama'a.

Kasar China ta kawo karshen tsauraran manufofinta na na kayyade haihuwa, wanda aka sanya a shekarar 1980 lokacin da take fargabar yawan al’ummarta za su ninka a shekarar 2016, sai dai daga bisani ta fara barin ma'aurata su haifi 'ya'ya uku a shekarar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.