Isa ga babban shafi

Biden na sha'awar ya gana da Zelensky a taron G7 a Hiroshima

Shugaban Amurka Joe Biden na fatan ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a taron G7 na Japan, bayan share fagen isar da jiragen yaki a nan gaba don taimakawa Ukraine ta 'kare kanta' daga  Rasha.

Shugaban Ukraine a taron G 7 na Japan  Volodymyr Zelenskiy
Shugaban Ukraine a taron G 7 na Japan Volodymyr Zelenskiy © via REUTERS - UKRAINIAN PRESIDENTIAL PRESS SERVICE
Talla

Fadar shugaban  Amurka ta bakin daya daga cikin ma'aikatan ta ya fada a yau asabar cewa an shirya taron na kasashen biyu  wato Ukraine da Amurka na gobe lahadi inda shugaban na Amurka "zai ci gaba da jaddada goyon bayan kasar sa ga Ukraine.

Shugaban na Amurka Joe Biden na fatan samun damar yin magana da  Zelensky kuma kai-da-kai, in ji mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan.

Shugaban UIkraine. Zelensky wanda ya je taron na G7 ya samu goyan bayan wasu daga cikin manyan kasashen Duniya musamman da firaministan Burtaniya Rishi Sunak, shugaban Faransa Emmanuel Macron da firaministan Indiya Narendra Modi.

Joe Biden ya  ce a shirye yake ya baiwa wasu kasashe damar baiwa Kiev jiragen yakin da Mista Zelensky ya dade yana bukata, samfurin F-16 na Amurka. Shawarar "tarihi", ta yaba wa shugaban Ukraine.

Yanzu Washington za ta goyi bayan wani shiri na hadin gwiwa da kawayenta suka yi na horar da matukan jirgin na Ukraine kan jiragen F-16.

A yayin wannan horon da ake sa ran za a dauki watanni, kasashen yammacin duniya za su yanke shawarar jadawalin jigilar jiragen da adadinsu da kuma kasashen da za su ba su, in ji Mista Sullivan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.