Isa ga babban shafi

Gobara ta kashe sama da dalibai 20 a kasar Guyana

Akalla mutane 20 ne suka mutu jiya Lahadi a wata gobara da ta tashi a dakin kwanan dalibai a Guyana, kamar yadda gwamnatin kasar ta tabbatar a cikin wata sanarwa da ta fitar, abinda shugaban kasar ya bayyana a matsayin bala'I mafi muni.

Mutane tsaye a cikin dakin kwanan daliban makarantar sakandare da suka kone, bayan da wasu yara da dama suka mutu.
Mutane tsaye a cikin dakin kwanan daliban makarantar sakandare da suka kone, bayan da wasu yara da dama suka mutu. via REUTERS - GUYANA PRESIDENCY
Talla

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta ce, adadin wadanda suka mutu ya kai 20, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi a makarantar sakandare ta Mahdia da ke tsakiyar kasar Guyana.

Shugaban kasar da ke yankin Kudancin Amurka, Irfaan Ali ya ce ya ba da umarnin shirin ko ta kwana manyan asibitocin Georgetown biyu da ke babban birnin kasar domin bai wa yaran kyakkyawar kulawa.

An aike da jiragen soji zuwa Mahdia, wanda ke da tazarar kilomita 200 kudu da Georgetown, saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin da aka yi.

Natasha Singh-Lewis, 'yar majalisar adawar kasar, ta yi kira da a gudanar da bincike kan musabbabin gobarar.

Guyana, karamar kasa ce mai magana da harshen turanci mai mutane 800,000, tsohuwar kasar Holland ce da Birtaniyya ta yi wa mulkin mallaka, kuma kasar na da arzikin man fetur, abin da take fatan zai taimaka wajen bunkasa ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.