Isa ga babban shafi

Ana bukatar Dala miliyan 333 domin taimakon mutanen Myanmar

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da asusun neman tallafin gaggawa na Dala miliyan 333 domin agaza wa mutane miliyan 1 da dubu 600 da suka gamu da ibtila’in guguwar Mocha a Myanmar.

Lokacin da guguwar Mocha ke kadawa.
Lokacin da guguwar Mocha ke kadawa. via REUTERS - PARTNERS RELIEF AND DEVELOPMENT
Talla

Guguwar ta Mocha mai tafe da ruwan sama da iska tare da gudun kilomita 195 cikin sa’a guda, ta afka wa Myanmar da Bangladesh ne a ranar 14 ga watan Mayun da muke ciki, inda ta rusa gidaje, sannan ta haddasa tumbatsar koguna da suka mamaye tituna.

Gwamnatin Mulkin Sojin Myanmar ta bayar da alkaluman mamata 148 da ta ce sun rasa rayukansu a sanadiyar ibtila’in kuma akasarinsu sun fito ne daga kabilar Rohingya a jihar Rakhine.

Yanzu haka Ofishin Kula da Al’amuran Jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, ana bukatar Dala miliyan 333 domin samar da matsuguni da magunguna da abinci da tsaftataccen ruwan sha ga mutanen da ibtila’in ya shafa.

Ana dai bukatar wannan agajin gaggawar ne kafin damuna ta kankama domin dakile yaduwar cututtuka tsakanin al’umma kamar yadda majalisar ta ce.

A bangare guda, mahukuntan Bangladesh sun ce, babu mutun ko guda da guguwwar ta yi sanadiyar ajalinsa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.