Isa ga babban shafi

Ko Recep Erdogan zai iya lashe babban zaben Turkiyya?

Yayin da aka shiga rana ta karshe na gudanar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasar Turkiya da za’a gudanar da zagaye na biyu a ranar Lahadi, ‘yan takara a zaben Recep Tayyip Erdogan da abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu, na ci gaba da nuna fargabar game da halin 'yan cirani da kuma mayakan Kurdawa ke ciki. 

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan © RFI / Marcia Bechara
Talla

Erdogan na neman ci gaba da mulkin kasar ne har zuwa shekarar 2028, sai dai ya na fuskantar kalubale daga wajen abokin hamayyar sa Kemal Kilicdaroglu. 

A wani jawabi da Kilicdaroglu ya gabatar a wajen gangamin yakin neman zabe, yayi alkawarin gudanar da gwamnati ta baidaya da inganta alakar kasar da kasashen yammaci da kuma magance matsalar tattalin arzikin kasar. 

Ya kuma kulla alaka da wasu jam’iyu 6, irin alakar da a baya Erdogan ya rinka yi wajen samun nasara, ga kuma goyon bayan Kurdawa da ya ke samu.  

Toh sai dai dan takarar da yazo na uku a zaben, Dinan Ogan ya sanar da goyon bayansa ga shugaba Recep Erdogan a zagaye na biyu na zaba da zai gudana a ranar lahadi. 

Janyewar ta Ogan zai taimakawa Erdogan a zagaye na 2 na zaben wanda ke matsayin karon farko a tarihi da Turkiya ke kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.