Isa ga babban shafi

Sharar robobi ya zama wani al'amari mai ba-tsoro a duniya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi gargadin cewa, gurbata muhallin duniya da sharar robobi wani al’amari ne mai ban-tsoro a daidai lokacin da jakadun kasashen duniya suka fara gudanar da taronsu na kwanaki biyar a birnin Paris da zummar dabbaka  yarjejeniyar magance matsalar gurbata muhallin da sharar robobin.

Sharar robobi na barazana ga muhallin duniya kamar yadda masana suka bayyana.
Sharar robobi na barazana ga muhallin duniya kamar yadda masana suka bayyana. Getty Images - Rosemary Calvert
Talla

Wakilan kasashen duniya 175 ne suka hadu a shalkwatan Hukumar Bunkasa Ilimi, Kimiya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya a wani taronsu na biyu daga cikin jerin taruka biyar da za su yi da zummar samar da ci gaba kan wata yarjejeniya mai cike da tarihi ta magance matsalar malalar sharar robobi.

Jim kadan da bude wannan zama, shugaban kulla yarjejeniyar, Gustavo Meza-Cuadra Velazquez ya ce, akwai kalubale babba a gabansu kamar yadda kowa ya sani, amma za su iya shawo kan matsalar a cewarsa.

Velazquez ya kara da cewa, yanzu haka hankulan kasashen duniya sun koma kansu, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashen da suka halarci taron da su kawo karshen tsarin masana’antar nan ta yadda kasashe mawadata ke safarar sharar robobi zuwa kasashe matalauta.

Shugaba Macron ya ce, sharar robobi wani al’amari ne mai ban-tsoro wanda tuni ya zama gagarumar matsala a duniyarmu ta yau.

Macron wanda ke magana ta kafar bidiyo, ya kara da cewa, makamashin da ke gurbata muhalli na barazana ga muradun magance matsalar sauyin yanayi da kuma lafiyar dan Adam har ma da zamantakwar da ke tsakanin halittu da muhalli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.