Isa ga babban shafi

Japan na fuskantar yanayin zafi mafi muni a tarihin kasar

Japan na fuskantar tsananin zafin da rabon da a ganshi a kasar tun 1898, wanda yanzu ya kai ma’aunin Celcious 34.9. 

Hukumar kula da yanayi ta kasar Japan ta yi gargadin cewa za a ci gaba da fuskantar tsananin zafi.
Hukumar kula da yanayi ta kasar Japan ta yi gargadin cewa za a ci gaba da fuskantar tsananin zafi. Saitama prefectural government/AFP
Talla

Bayanai sun ce tuni aka ragewa ma’aikatan tsahon lokutan aikin su, haka kuma an kulle makarantu a wasu sassan kasar saboda tsananin zafin da ya fara daga watan Maris zuwa Mayun da ya gabata. 

Wannan na kara nuna irin illar da sauyin yanayi ke yiwa kasashen duniya, bayan annobar ambaliyar ruwa da aka rika gani a wasu kasashe da aka rika fuskanta a watannin baya. 

Kasashe da dama, musamman matalauta wadanda aka barsu a baya kan shrin allurar rigakafin Korona sun bayyana damuwa kan illolin da sauyin yanayi ya haifar musu.

A halin yanzu dai, dumamar yanayin duniya kan ma’aunin Celsius na da maki 1.1 ne, kuma ana ganin wannan lamari na da nasaba da musibun da suka afka wa wasu kasashen duniya a baya-bayan nan, kamar Canada wadda ta yi fama da mugun zafi da kuma China da Jamus da suka gamu da gagarumin ibtila’in ambaliyar ruwa, sai kuma  wuatar daji  da ta addabi Girka da California.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.