Isa ga babban shafi

Fasahar AI za ta haddasa karuwar take hakkin dan adam- Kwararru

Kafin zuwan fasahar AI ko kuma Artificial Intelligence wadda aka sanyawa basirar dan adam don bai wa na’urori damar yin ayyukan da jama’a kan iya yi koma fiye, akwai fasahohin da ake amfani da su kama daga wayar salula ko kuma agogunan zamani da ake sanyawa manhajar gano inda mutum ya ke don bibiyarsa, fasahar da ke gamuwa da suuka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam musamman a lokacin zanga-zanga ko kuma bore ga gwamnatoci.

Fasahar AI na ci gaba da samun karbuwa a sassan daban daban na Duniya.
Fasahar AI na ci gaba da samun karbuwa a sassan daban daban na Duniya. CC0 Creative Commons
Talla

Duk da yadda aka samu gagarumin ci gaba wajen samar da wannan fasaha ta bibiya, masana na ganin barin wayoyi ko agogo a gida yayin shiga irin wannan gangami zai taimaka matuka wajen dakile gwamnatoci daga take hakkin dan adam, yayinda zuwan fasahar AI za ta kara bai wa irin wadannan gwamnatoci damar take hakkin jama’a a cewar kwararru a bangaren zamantakewa.

Dr Mona Sloane babbar jami’ar binciken kimiyya a jami’ar birnin New York guda cikin manyan cibiyoyin da suka taimaka wajen samar da fasahar ta AI kuma kwararriya a fannin zamantakewa wadda yanzu haka ke aikin nazartar zubin fasahar ta AI da kuma gudunmawarta ga al’umma, ta ce dole akwai bukatar fadada bincike kan tasirin da wannan fasaha za ta yi ga zamantakewar dan adam.

A cewar Sloane ita wannan na’ura an sanya mata fikirar iya yanke hukunci ko saukaka aiwatar da hukuncin fiye da dan adam sai dai akwai gazawa cikin bayanan da ke kunshe cikinta ko kuma bayanan da aka kimsa mata.

Kwararriyar ta bayyana cewa lura da yadda za a koma amfani da na’urori masu basirar AI gadan-gadan, akwai bukatar tsananta bincike kan tasirin da za ta yi wajen dakile walwala ko kuma take hakkin dan adam dama dukkanin mu’amalar da za ta shiga tsakaninta da jama’a.

A cewar Sloane akwai amannar cewa idan har aka sanyawa na’urorin masu fasahar AI dukkanin bayanan da suka kamata za su taimaka wajen dakile cin zarafi sabanin hakan kuma zai sake haddasa tarnaki ga masu bore ko bijirewa gwamnatoci lura da yadda cikin sauki za a iya bin diddiginsu fiye da yadda ake yi da wayoyin salula ko fasahohin da ake amfani da su a yanzu.

Dr Mona Sloane ta gwada misali da yadda mahukuntan Hong Kong suka yi amfani da wayoyin salula da kuma agoguna na zamani masu dauke da fasahar bin diddigi da ke matsayin wani bangare na fasahar ta AI wajen gano wadanda suka shiga boren tare da hukunta su duk da yadda suka rufe fuskokinsu, batun da jami’ar ke cewa ya zama wajibi mutane su ankare.

Ko a baya-bayan nan, sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam irinsu Amnesty International suka soki salon amfani da na’urar mai dauke da fasahar tantance fuskokin jama’a wajen nadar bayanan wadanda suka shiga bore ko kalubalantar gwamnatoci wanda ta ce sun sabawa ‘yancin dan adam da kuma dokokin fadar albarkacin baki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.