Isa ga babban shafi

Kamfanin IndiGo ya kafa tarihin ciniki mafi girma a bajekolin jiragen sama

Kamfanin sufurin jiragen saman IndiGo na kasar India ya sanar da kulla yarjejeniyar sayen jiragen sama kirar A320 500 daga kamfanin kera jiragen saman Airbus mallakar kasashen Turai.Wannan shine ciniki mafi girma da aka taba gani a tarihin bikin baje kolin jiragen saman da ake yi a Le Bouget dake birnin Paris. 

Kamfanin sufurin jiragen saman IndiGo na kasar India ya sanar da kulla yarjejeniyar sayen jiragen sama kirar A320 500 daga kamfanin kera jiragen saman Airbus mallakar kasashen Turai.
Kamfanin sufurin jiragen saman IndiGo na kasar India ya sanar da kulla yarjejeniyar sayen jiragen sama kirar A320 500 daga kamfanin kera jiragen saman Airbus mallakar kasashen Turai. © REUTERS/Vivek Prakash
Talla

A ranar farko ta kadamar da bikin baje kolin jiragen sama da kayayyakin yakin da kamfanoni sama da 2500 ke baje hajjarsu, kamfanin jiragen saman IndiGo na kasar India ya sanar da kulla wannan yarjejeniyar ta sayen jiragen saman da kudin su ya kai Dala biliyan 55, wanda ake saran a kammala kera su tsakanin shekarar 2030 zuwa 2035. 

Idan an kammala kera jiragen, adadin jiragen kamfanin IndiGo zai kai akalla 1,230, yayin da abokin gogayyar sa na Air India yayi irin wannan odar ta jirage 470 a watan Fabarairun shekarar 2022 akan farashin Dala biliyan 70. 

Shugaban kamfanin IndiGo Peter Elbers ya bayyana yarjejeniyar sayen jiragen a matsayin gagarumar ci gaba a gare su da kuma kamfanin Airbus. 

Tsaiko da annobar korona ta haifar

Wannan shine karo na farko da ake gudanar da bikin baje kolin jiragen saman da kuma kayayyakin yaki a cikin shekaru 4 da suka gabata, sakamakon annobar korona wadda ta tilasta dakatar da bikin a shekarar 2021. 

Rikicin Ukraine ya baiwa kasashen duniya da damar zuwa wajen bikin baje kolin domin sayen jiragen yaki da kuma sabbin makaman zamani da ake baje kolinsu a Le Bourget dake Faransa. 

A wannan shekarar, shugabannin dake shirya bikin sun ce, kamfanoni sama da 2,500 suka baje hajarsu da ta kunshi sabbin jiragen sama na fasinja da jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu da masu sarrafa kansu da kuma tasi masu tashi sama. 

Jirgin sama mara gurbata muhalli

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bude bikin wajen amfani da jirgin saman da baya gurbata muhalli da kamfanin Airbus ya kera da ake kira A321 XLR, yayin da jiragen helicopter da jiragen kai harin soji suka y ita shawagi. 

Ana saran baki daga kasashen duniya dubu 320 su halarci bikin na mako guda, cikin su harda jami’na soji da fararen hula domin ganewa idanun su irin sabbin makaman da aka samar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.