Isa ga babban shafi

Sojojin Wagner sun dakatar da yunkurin afkawa birnin Moscow

Sojojin hayan Wagner wadanda suka mamaye mafi yawan hanyar zuwa birnin Moscow sun amince da janye aniyar su ta tunkar birnin da suka yi don gujewa zubar da jini, kamar yadda shugabansu Yevgeny Prigozhin ya sanar, a wani mataki na dakile abin da ya zama babban kalubale ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

Sojojin Wagner akan babbar hanyar M-4, wacce ta sada birnin Moscow da kudancin kasar.
Sojojin Wagner akan babbar hanyar M-4, wacce ta sada birnin Moscow da kudancin kasar. REUTERS - STRINGER
Talla

Tun da farko dai, dakarun na Wagner sun tunkari birnin Moscow ne gadan-gadan domin gwamnan yankin Lipetsk da ke kasar Rasha Igor Artamonov, ya ce sojojin haya na Wagner sun iso yankin shi tare da makamansu, a hanyar su ta isa babban birnin kasar Moscow, wanda bai wuce tazarar kilomita 400 ba, don kwace ikonsa daga sojojin kasar.

A sanarwar da gwamnan ya wallafa a Telegram, ya bukaci al’ummar yankin su ci gaba da zama a gidajensu, sannan kar su kar suyi wani yunkurin tafiya ko ina.

Shi dai yankin Lipetsk na kusa da birnin Moscow fiyeda na Voronezh, wanda da sanyin safiyar asabar din nan sojojin Wagner suka kwace ikon duk wasu wurare na sojojin Rasha.

Matakin kare birnin Moscow

A cewar wasu hotuna da jaridar Vedomosti ta wallafa, sojojin Rasha sun jibge manyan bindigu masu sarrafa kansu a shiyar kudu maso yammacin birnin Moscow, ya yinda kuma ‘yan sanda suka taru a babbar hanyar M4 wacce ta nan ne ake saran sojojin Wagner zasu bullo.

Haka nan magajin garin Moscow Sergei Sobaynin, ya bukata mazauna birnin su takaita zirga-zirga, ta re da bayyana ranar Litinin a matsayin hutu.

Me cece aniyar Wagner

Shugaban sojojin hanar Wagner Yevgeny Prigozhin.
Shugaban sojojin hanar Wagner Yevgeny Prigozhin. AP

 

Shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner Yevgeny Prigojine ya ce ya koma cikin kasar Rasha tare da dakarunsa daga yankunan Ukraine, inda ya sha alwashin kawar da rundunar sojin kasar, yana mai cewa a shirye yake ya mutu tare da sojojinsa kimanin 25,000 domin 'yantar da al'ummar Rasha.

Martanin kasashe

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce ya gana da takwarorin sa na kungiyar G7.

Blinken ya sake jaddada aniyar Amurka na tallafawa Ukraine a yakin da take yi da Rasha.

A nashi bangaren, shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiya, a yayin wata ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ta waya, ya ce Turkiya za ta yi duk abinda ya kamata don sasanta matsalar da ke faruwa a Rasha, duk da dai sanarwar da fadar Kremlin ta fitar ta ce Erdogan ya bayyana goyon bayansa ne ga Putin.

Tuni itama ma’aikatar kulada harkokin kasashen wajen Iran ta fitar da sanarwar da ta ce, abinda ke faruwa a Rasha matsala ce ta cikin gida, amma tana tare da Rasha wajen tabbatar da doka da oda a cikin kasarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.