Bikin Sallar Layya cikin hotuna
Miliyoyin al'ummar Musulmin duniya na gudanar da shagulgulan bikin babbar salla a sassan duniya, inda suke ziyarce-ziyarce don sada zumunci a tsakaninsu da kuma girke-girke har ma da yanke-yanken dabbobi irinsu raguna da shanu da rakuma.
Wallafawa ranar: 28/06/2023 - 22:02
Minti 2
Karamar yarinya a birnin Manila na kasar Philippines dauke da daddumai a kanta. REUTERS - LISA MARIE DAVID
Wasu 'yan uwan juna kenan da ke daukar hoto bayan saukowa daga sallar idi a birnin New York na Amurka. REUTERS - AMR ALFIKY
Dimbin Musulmai kenan a lokacin da suke sallar idi a birnin Mogadishu na Somalia. REUTERS - FEISAL OMAR
Ana shirin fara yankar raguna a birnin Abidjan na Ivory Coast. REUTERS - LUC GNAGO
Wata budurwa na nuna lallen da ta yi don adon salla a Abidjan na Ivory Coast. LG - LUC GNAGO
Wasu Musulmai a kauyen Kok na kasar Kyrgystan suna gudanar sa sallar idi. REUTERS - VLADIMIR PIROGOV
Musulman birnin New York na Amurka na murnar bikin sallar layya. REUTERS - AMR ALFIKY
Falasdinawa kenan a lokacin da suke yanka dabbar layya. REUTERS - IBRAHEEM ABU MUSTAFA
Wata karamar yarinya a birnin New York da ke kwalliyar da zanen furanni a fuskanta a ranar salla. REUTERS - AMR ALFIKY
Musulmai a Philippines na shirya girkin sallar layya REUTERS - LISA MARIE DAVID
Zurfafa karatunka kan maudu'ai iri guda: