Isa ga babban shafi

Sabuwar manhajar Threads na barazana gaTwitter

Sama da mutane miliyan 30 sun yi rajistar fara amfani da sabuwar Manhajar Threads ta Kamfanin Meta a ranar farko da aka kaddamar da ita  kamar yadda shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ya sanar.

Sabuwar manhajar Threads na barazana ga Twitter
Sabuwar manhajar Threads na barazana ga Twitter © AP/Richard Drew
Talla

Ana kallon sabuwar manhajar tamkar kishiya ga dandalin sada zumunta na Twitter da attajirin nan Elon Musk ya saye a cikin watan Oktoban da ya gabata.

Manhajar dai ta tafi kai-tsaye a rumbun Apple da Android a kasashen duniya 100 da misalin karfe 11 na dare agogon GMT a ranar Larabar da ta gabata.

Masana Harkokin Sadarwa sun ce, sabuwar manhajar ta Threads za ta iya janyo hankulan masu amfani da Twitter musamman saboda rashin gamsuwa da wasu sauye-sauye da dandalin ya yi a baya-bayan nan.

Kodayake kamfaanin Twitteer ya ce,  duk da cewa, ya taikata wasu abubuwa , amma babu wani dandali da zai tara irin jama’ar da ke amfani da shi.

Ita dai sabuwar manhajar ta Threads na bai wa masu amfani da ita damar wallafa haruffa 500, sannan tana kamanceceniya da Twitter a bangarori da dama.

Daga cikin fitattun mutanen da suka fara amfani da Threads har da Jennifer Lopez da Shakira da Hugh Jackman, sai kuma wasu manyan kafafen yada labarai na duniya irinsu The Washington Post da The Economist.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.