Kasashe 140 sun cimma matsaya kan karbar haraji daga kamfanoni na duniya
Kusan kasashe 140 ne suka dauki matakin farko don cimma yarjejeniya kan yadda za a raba kudaden harajin da ake samu daga kamfanoni na kasa da kasa, in ji kungiyar bunkasa tattalin arziki ta duniya ta OECD.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wasu kasashe 138, wadanda ke da sama da kashi 90 cikin 100 na abin da ake fitarwa na tattalin arzikin duniya, sun amince da daftarin farko na yarjejeniyoyin bangarori daban-daban kan yadda za a rika biyan harajin wadannan kamfanoni da ke gudanar da ayyukansu a duk fadin duniya, biyo bayan tattaunawar kwanaki biyu da kungiyar ta shirya a Paris.
Kamfanoni da yawa, musamman kamfanonin fasaha, a halin yanzu suna iya sauya hanyoyin rubanya riba cikin sauki ga kasashen da ke da karancin haraji.
A yarjejeniyar da OECD ta jagoranta a shekarar 2021, an cimma matsaya kan mafi karancin haraji na kashi 15 bisa 100 kan kasashen duniya da kuma samar da ka'idoji kan yadda za a rika biyan harajin kasashe daban-daban, ta yadda kasashe ba za su yi asara ba.
Amma OECD ta ce matasayar da aka cimma a wannan makon ya ba da damar samar da ci gaba tare da mai tarihi, gat sarin haraji na duniya.
Kasashen sun kuma yi alkawarin amfani da sabbin tsarin dijital a bangaren haraji kafin Disamba 2024 ko kuma fara aiki da yarjejeniyoyin da aka cimma a babban taron na duniya, muddin aka samu hadin gwiwa mutunta matsayar da aka cimma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu