Isa ga babban shafi

Rasha ta kakkabo wani jirgin yakin Ukraine a Belgorod

Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, dakarun tsaron saman kasar sun lalata wani jirgin sama mara matuki da Ukraine ta harba a yankin Belgorod da sanyin safiyar Lahadi.

Wasu sojojin Ukraine kenan da ke filin daga, kusa da Kharkiv ranar 7 ga watan Afrilun 2022.
Wasu sojojin Ukraine kenan da ke filin daga, kusa da Kharkiv ranar 7 ga watan Afrilun 2022. AP - Andrew Marienko
Talla

Ma'aikatar ta ce ba a samu asarar rai ko barna da harin ya haddasa ba.

Yankin Belgorod da ke kudancin Rasha yana iyaka da ne da kasar ta Ukraine.

Wannan ya zo ne, bayan wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Biritaniya ta fitar, da ke cewa akwai yuwuwar cewa Rasha ta daina tallafawa ayyukan sojojin haya na kamfanin Wagner.

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce gwamnatin kasar Rasha ta dauki matakin sabawa wasu muradun kasuwanci na mamallakin kamfanin Wagner, Yevgeny Prigozhin, bayan da ya jagoranci wani harin ta'addanci da bai yi nasara ba a kan manyan sojojin Rasha a watan Yuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.