Isa ga babban shafi

Vladimir Putin ba zai halarci taron kungiyar BRICS ba

Kungiyar kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa ta BRICS ta sanar da cewa shugaban Rasha Vladimir Putin ba zai halarci taron kungiyar na wannan wata da zai guda a Afrika ta Kudu ba.

Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Shugaban Rasha Vladimir Putin. AP - Mikhail Metzel
Talla

A mako mai zuwa ne ake sa ran za a kaddamar da taron kungiyar da zai mayar da hankali kan yadda tattalin arzikin duniya ke tafiya da kuma hanyoyin da za a bi wajen samar da daidaiton tattalin arziki a tsakanin kasashen duniya.

Taron na bana zai kuma duba hanyoyin da za a bi wajen rage irin tasirin da kasashen yammacin duniya ke da shi wajen tafiyar da tattalin arzikin duniya, wanda hakan ke yi wa kasashe musamman ‘yan rabbana-ka-wadata-mu illa.

Bayanai sun nuna cewa  Putin na Rasha ba zai halarci taron ba, don guje wa kamun kotun duniya wadda ke shirin kama shi da zarar ya jefa kafarsa a Afrika ta Kudu a sakamakon zargin sa da aikata laifukan yaki a Ukraine, kasar da yake yaki da ita.

Tun kafin yanzu dai kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bukaci shugaban Afrika  ta Kudu ya mika mata Putin da zarar ya shiga kasar kasancewarta mamba a kotun ta duniya, sai dai kuma ana ganin hakan ba abu ne mai yiwuwa ba, saboda kyakkyawar alakar da ke tsakanin Rasha da Afrika ta Kudu.

Wannan dalilin ne ya sa, tun farkon watan shekaran-jiya, kotun ta sanar da aike wa da wakilin ta kasar Afrika ta Kudun, wanda kuma aka dora masa alhakin kama mista Putin.

Kawo yanzu, an tabbatar da halartar shugaban kasar China Xi Jingping da na Brazil Lula da Silver da kuma firaministan India Narendra Modi, inda za su samu tarbar shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.