Isa ga babban shafi

Zababben shugaban Guatamala na zargin shirya masa juyin mulki

Zababben shugaban kasar Guatemala Bernardo Arevalo ya yi Allah wadai da juyin mulkin da hukumomin kasar ke yukurin yi na hana shi karbar mulki, bayan da aka dakatar da jam'iyyarsa ta siyasa.

Zababben shugaban Guatamala kenan, Bernardo Arevalo.
Zababben shugaban Guatamala kenan, Bernardo Arevalo. AP - Moises Castillo
Talla

 

Arevalo, mai shekaru 64 masanin ilimin zamantakewa, ya tsallake rijiya da baya, inda ya lashe zaben ranar 20 ga watan Agusta, tare da shan alwashin murkushe masu satar dukiyar jama'a, lamarin da masu lura da al'amura ke cewa ya firgita masu cin hanci da rashawa.

A ranar Litinin ne aka ayyana Arevalo a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 58 na kuri'u, amma kotun zaben ta dakatar da jam’iyyarsa ta Semilla.

Arevalo ya samu nasarar tsallakewa zagaye na biyu bayan bayan alwashin da ya sha na kawo karshen talauci, tashin hankali, da cin hanci da rashawa da tilastawa dubban ‘yan kasar yin kaura zuwa kasashen ketare duk shekara domin neman ingantacciyar rayuwa.

A makon da ya gabata, Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Amurka mai hedkwata a Washington ta ce Arevalo da mataimakinsa Karin Herrera na fuskantar cin zarafi, bayyana bayanan sirrisu ga jama'a ta kafofin yada labarai, da kuma barazanar da suka hada da yunkurin kasha su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.