Isa ga babban shafi

Ministan tsaron Ukraine ya mika takardar barin aiki

Ministan tsaron Ukraine Oleksii Reznikov ya mika takardar yin murabus a ranar Litinin bayan da shugaban kasar Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa ma'aikatarsa na bukatar sabbin hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen kalubalen da kasar ke fuskanta.

Oleksii Reznikov  kenan
Oleksii Reznikov kenan © via REUTERS / UKRAINIAN PRESIDENTIAL PRESS SER
Talla

Sauyin shugabancin ya biyo bayan zarge-zargen cin hanci da rashawa da dama a cikin ma'aikatar tsaron kasar.

"Na mika wasikata ta murabus ga Ruslan Stefanchuk, shugaban majalisar dokokin Ukraine. Abin alfahari ne na yi hidima ga al'ummar Ukraine da kuma yin aiki ga sojojin kasata na tsawon watanni 22, lokacin da ya kasance mafi tsanani a tarihin Ukraine," in ji Reznikov.

Zelensky ya ce ya yanke shawarar maye gurbin ministan tsaronsa, wanda shi ne mataki mafi girma da aka samu tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a watan Fabrairun 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.