Isa ga babban shafi

Farashin shinkafa ya yi tashin fiye da shekaru 15 a kasuwannin Duniya- FAO

Hukumar bunkasa harkokin noma ta majalisar dinkin duniya ta sanar da tashin farashin shinkafa mafi kai wa kololuwa cikin shekaru 15 a watan da ya gabata na Agusta wanda ta alakanta da matakin India na haramta fitar da shinkafar ketare a watan Yulin da ya gabata.

Hukumar FAO ta ce tashin farashin shinkafar na da nasaba da matakin India na haramta fitar da shinkafa daga kasar.
Hukumar FAO ta ce tashin farashin shinkafar na da nasaba da matakin India na haramta fitar da shinkafa daga kasar. AP - Heng Sinith
Talla

A rahoton wata-wata da FAO kan fitar, ta ce duniya ta ga mafi kololuwar tsadar shinkafa a watan Agusta wanda ya hauhawa da kashi 9.8 idan na kwatanta da yadda aka sayar da shinkafar a watan Yuli, batun da hukumar ke cewa ya biyo bayan matakin mahukunta India na haramtawa kamfanin Indica fitar da nau’in farar shinkafa kasashen ketare.

Hukumar ta FAO ta ce rashin tabbas game da tsawon lokacin da wannan haramci na India zai dauka, ya tilastawa masu hada-hadar shinkafar sauya kaso mai yawa na yarjejeniyar cinikayyar da ke tsakaninsu da ‘yan kasuwa ko kuma dakatar da tallata kayakin nasu dama sanya farashin kan kayan da suke da shi a hannu.

A cewar hukumar wannan dalili ya sanya raguwar hada-hadar shinkafar duk kuwa da tsananin bukatar ta da ake da shi kasancewar ta nau’in abinci da kaso mai yawa na Duniya ya dogara da shi, lamarin da ya sanya hauhawar farashin mafi kololuwa da Duniya ta gani cikin shekaru 15.

India wadda ke samar da kashi 40 na yawan shinkafar da Duniya ke bukata, a watan Yuli ne ta sanar da haramta fitar da nau’in farar shinkafa zuwa kasuwannin duniya saboda tabbatar da wadatuwarta a cikin kasa, ko da ya ke ta bayar da damar fitar da shinkafar nau'in Basmati mai daraja.

Wannan haramci na India tuni ya haddasa mummunar illa ga kasashen Afrika da Turkiya baya ga Syria da kuma Pakistan wadanda dama dukkaninsu ke fama da matsalar hauhawar farashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.