Isa ga babban shafi

Shugabar kungiyar tarayyar turai Ursula Von der Layen ta Ziyarci yan ci ranin Lampedusa

A wannan lahadin ce, Shugabar komitin zartarwar kungiyar tarayyar turai uwargida Ursula Von der Layen ta ziyarci tsibirin Italiya na  Lampedusa, inda dubban ‘yan ci rani suka isa a makon da ya gabata, al’amarin da ya sake farfado da zazzafar mahawarar neman raba nauyin kula da su  tsakanin kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turai.

Des migrants arrivés à Lampedusa attendant d'être transféré en Italie continentale, le 15 septembre 2023.
Des migrants arrivés à Lampedusa attendant d'être transféré en Italie continentale, le 15 septembre 2023. © Cecilia Fabiano / AP
Talla

Matsalar yan ci ranin da ta shafi tsibirin Lampedusa na kasar Italiya a cikin kwanakin ukun da suka gabata,  ta haifar da gagarumin aikin karakainar diflomasiya. Haka kuma ta zama kan gaba  a tattaunawar wayar telefon da aka yi a ranar assabar 15 ga watan satumba 2023 tsakanin shugaban Faransa  Emmanuel Macron, da  Firaministan Italiya uwargida Giorgia Meloni.

Shugaban Faransa da shugabar gwamnatin Italiya sun dau niyar ganin sun karfafa huldar dake tsakanin kasashen turai, domin samar da masalaha mai inganci, ga wannan dadaddiyar matsala ta yan ci rani  da taki ci ta ki ciyewa .

Haka kuma shuwagabanin biyu, sun bayyana batun aikin hadin guiwa tsakanin  Faransa da Itali a gabar ruwan ta tekun  na Méditerranien, kamar yadda a fadar shugabancin kasar Faransa ta Élysée ta sanar, ba tare da yin wani karin haske ba kan yadda huldar aikin zata gudana tsakanin kasshen biyu.

Har ila yau an gudanar da tattaunawar wayar telefon  tsakanin ministocin cikin gidan Faransa, Itali, Jamus, da kuma wakilin shugaban kasar Spain, da  kungiyar tarayyar turai, hade da komishinan cikin gidan kungiyar tarayyar turai  Ylva Johansson.

Ministan cikin gidan faransa Gérald Darmanin ne, ya gabatar da shawarar tattaunawa   tare da takwaransa na Italiya, Matteo Piantedosi, da ta kasar Jamus, Nancy Faeser. Sai dai babu abinda ya fito daga tattaunawar ta su.

Shugabar gudanarwar kungiyar tarayyar turai uwargida Ursula von der Leyen kai tsaye a wannan lahadi 17 ga watan satumba 2023 tare Firaministan Italiya  Giorgia Meloni, a jiya sun bukaci saka batun yan  ci rani daga cikin batutuwan da za’a tattauna a lokacin babban zaman taronda  kungiyar tarayyar turai zata gudanar a cikin watan octobar wannan shekara ta 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.