Adadin wadanda suka mutu ya haura dubu daya a Isra'ila
Isra'ila ta sanar da soma yaki da kungiyar Hamas a hukumance, bayan farmakin da ba a taba ganin irinsa ba da kungiyar Islama ta Falasdinu ta kaddamar daga Gaza, wanda adadin wadanda suka mutu ya haura dubu daya.
Wallafawa ranar:
A ci gaba da neman sake kwace iko bayan wannan kazamin hari daga 'Yan kungiyar Hamas,sojojin Isra'ila sun ci gaba da zakulo 'yan kungiyar Hamas a kudancin Isra'ila tare da ci gaba da kai hare-hare ta sama kan wasu wurare a Gaza.
Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi kashedi yan lokuta biyo bayan wannan hari wanda ya yi sanadin mutuwar kusan dubu daya a cikin kasa da sa'o'i 48.
Fiye da mutane 600 aka kashe a Isra'ila tare da raunata 2,000, ciki har da 200 "a cikin mawuyacin hali", a wata sanarwa daga gwamnatin Isra’ila.
Kakakin rundunar sojojin Isra'ila da yammacin yau Lahadi ya na mai cewa suna tabbacin cewa mayakan Hamas na nan cikin tareda jama’a, jami’in ya kuma da yin alkawarin farautar "'yan ta'adda a duk inda za su kasance".
Sojojin Isra'ila sun aike da Karin dakaru da nufin sake samun cikakken ikon yankunan da yan kungiyar Hamas ke iko a kai a zirin Gaza, tare da kubutar da Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu