Isa ga babban shafi
FARANSA

Shugaban Faransa ya yi tir da harin ta'addancin da aka kai arewacin kasar

Shugaban Faransa, Emmauel Macron, ya yi tir da harin ta'addancin da aka kai wata makaranta da ke arewacin kasar, abin da ya yi sanadin mutuwar wani malami, tare da jikkatar wasu.

'Yan sandan Faransa kenan, lokacin da suka kai dauki makarantar da aka kai hari da ke arewacin Faransa, ranar 13 ga watan Oktoba, 2023.
'Yan sandan Faransa kenan, lokacin da suka kai dauki makarantar da aka kai hari da ke arewacin Faransa, ranar 13 ga watan Oktoba, 2023. © REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Macron wanda ya ce an samu nasarar dakile makamancin harin a wani yanki na kasar, za a kara tsaurara matakan tsaro da kuma fadada aiki binciken bayanan sirri.

Da safiyar ranar Juma'a ne, wani matashi ya kashe malami a makarantar sakandiren tare da raunata wasu na daban.

Matashin wanda ya kasance tsohon dalibin makarantar ne mai suna Mohammed Mogouchkov mai shekaru 20, an tsare shi yanzu haka, tare da kaddamar da binciken ta’addanci a kan sa.

Shugaba Macron, ya ce malamin ya rasa ransa ne a daidai lokacin da yake kokarin kare rayukan da ke wurin da al'amarin ya faru.

Rahotanni sun ce mai gadin makarantar tare da wani malami sun samu munanan raunuka sakamakon harin da matashin ya rika kai masa da wuka.

Mutumin da aka kashe wani malamin koyar da harshen Faransanci ne da aka kai wa hari a kofar shiga harabar makarantar.

Sashen da ke yaki da ta'addanci tuni ya dauki nauyin gudanar da bincike kan lamarin, bayan sun cafke shi tare da dan ‘uwansa mai shekaru 16.

Kafofin yada labaran Faransa sun ce Mogouchkov dan kasar Chechen ne, haifaffen kasar Rasha, inda ya shiga makarantar yana ihu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.