Isa ga babban shafi

Faransa za ta samar da asibiti a Masar don kula da majinyatan Gaza

Faransa na tattaunawa da Masar don samar da asibitin soji a ciki kasar, wanda zai rinka duba mutan Zirin Gaza da suka samu munanan raunuka ciki harda gudanar da tiyata, kamar yadda ministan tsaron Faransa Sebastien Lecornu ya bayyana.

Shugabn Faransa Emmanuel Macron tare ministan tsaron kasar Sebastien Lecornu.
Shugabn Faransa Emmanuel Macron tare ministan tsaron kasar Sebastien Lecornu. © REUTERS / STEPHANIE LECOCQ
Talla

A cikin wannan makon ne dai Paris za ta karbi bakuncin taron jin kai na kasa da kasa ga fararen hulan Gaza, a daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da kokarin kawo karshen yakin Hamas da Isra'ila.

"Akwai tattaunawa da muke yi da Masar domin gabatar da wani tayin samar da asibitin sojan Faransa, wanda zai maida hankali musamman wajen yin tiyata ga wadanda suka jikkata”.

Itama Masar ta samar da wani asibiti a Sheikh Zuweid da ke da nisan kilo mita 15 daga iyakar Rafah, da ake amfani da ita wajen fito da wadanda suka jikkata daga Gaza.

Faransa ta aike da jirgi mai saukar ungulu zuwa yankin, wanda shugaba Emmanuel Macron ya ce anyi hakan ne da nufin tallafawa asibitocin Gaza da kayan aikin.

Haka nan sojojin Faransa na shirin sake turawa da wani jirgi mai saukar ungulu yankin a karo na biyu, da ke dauke da kayan kiwon lafiya na zamani nan da kwanaki 10 masu zuwa.

Taron da za a yi a birnin Paris a ranar 9 ga wannan watan na Nuwamba, wanda zai tattauna batun kai kayan agaji, zai kuma duba batun samar da wata hanya ta teku, da za a yi amfani da ita wajen kai kayayyakin agaji zuwa Gaza, sannan kuma ana duba yadda za a yi amfani da jiragen ruwa wajen taimakawa wadanda suka jikkata da aka kwaso daga Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.