Isa ga babban shafi

Shugabannin hukumomin MDD sun bukaci gaggauta tsagaita wuta a Gaza

Shugabannin baki dayan hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana bacin rai kan yadda Isra’ila ke ci gaba da halaka fararen hula Gaza, wadanda a jimlace adadinsu ya zarce Falasdinawa dubu 10.

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York.
Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York. AP - Mary Altaffer
Talla

Cikin sanarwar da ba kasafai suka saba fitar da irinta ba, inda suka bukaci a gaggauta tsagaita wutar yakin Isra’ila da Hamas, shugabannin hukumomin na Majalisar Dinkin Duniya guda 18, ciki har da na UNICEF da WFP sun ce:

Kusan wata guda kenan kasashe sun zura ido sun kallon lamurran da ke wakana a yankin Falasdinawa da kuma Isra’ila, yayin da a lokaci guda dubban rayuka ke salwanta, wasu dubun dubatar kuma suke tagayyara.

Kusoshin Majalisar Dinkin Duniyar sun bayyana kisan fararen hula a Gaza gami da datsewa, ragowar Falasdinawan yankin samun ruwa da abinci da magunguna da kuma wutar lantarki, a matsayin wuce gona da iri, wanda kuma ba za a lamunta ba.

Hare-hare kan asibitoci

Sanarwar ta kara da cewa ya zuwa yanzu, haren-haren bama-bamai sama da 100 Isra’ila ta kai kan asibitoci a sassan Zirin Gaza, inda rayukan jami’an lafiya da sauran ‘yan gaji masu yawan gaske suka salwanta, cikinsu kuma har da jami’ai 88, na hukumar kula da Falasdinawa ‘yan gudun hijira.

Alkaluman da ma’aikatar lafiyar yankin Gaza ta fitar a baya bayan, sun nuna cewar Falasdinawa dubu 10,022 Isra’ila ta kashe, tun bayan hare-haren ramuwar da ta kaddamar kan harin da mayakan Hamas suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe mutane fiye da dubu 1,400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.