Kasashen duniya sun gaza shawo kan matsalar sauyin yanayi
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasashe na gazawa wajen daukar matakan shawo kan matsalar sauyin yanayi, sakamakon yadda nazarin da ta yi a game da alkawuran da suka dauka na rage hayaki mai gurbata muhalli na nuni da cewa ci gaban da aka samu dan kalilan ne.
Wallafawa ranar:
A wani rahoton da ta fitar ‘yan makwanni gabanin gagarumin taron da ke tafe a kan yanayi, hukumar kula da abin da ya shafi yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce duniya ta gaza wajen daukar matakan gaggawa don ganin bayan hayaki mai gurbata muhalli.
Ganin yadda yanayi ke kara zafi, kuma ake sa ran shekarar 2023 ta kasance mafi zafi a tarihin duniya, masana kimiyya sun ce dole ne a kara matsa wa shugabannin manya kasashen duniya don kawar da hayaki mai gurbata yaanayi.
Majalisar Dinkin Duniya ta gano cewa shirin da kasashe kusan 200 suka yi a game da saukaka dumamar yanayi zai rage hayaki mai gurbata yanayi a shekarar 2030 da kaso 2 ne kawai idan aka kwatanta da hekar 2019.
Shugaban kwamitin da ke nazari a batutuwan da suka shafi dumamar yana yi na Majalisar Dinkin Duniya, Simon Stiell ya ce duniya ta kauce hanya a game da rage dumamar yanayi, saboda haka taron yanayi na COP 28 da za a yi a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa ne dama ta kawo sauyi a wannan lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu