Isa ga babban shafi

Adadin fafaren hular da suka mutu a yakin Ukraine ya haura 10,000 - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, sama da fararen hula 10,000 ne suka mutum, tun daga lokacin da Rasha ta fara yaki a Ukraine a shekarar 2022.

Ma'iakatn kashe gobara kenan na kasar Ukraine, yayin da suke bakin, bayan wani harin sama da Rasha ta kai a yankin Lviv, ranar 19 ga watan Satumba, 2023.
Ma'iakatn kashe gobara kenan na kasar Ukraine, yayin da suke bakin, bayan wani harin sama da Rasha ta kai a yankin Lviv, ranar 19 ga watan Satumba, 2023. © AP
Talla

Ofishin kare hakkin dan adam na Majalisar da ke Ukraine, ya bayyana cewa a binciken da ma’aikatansa suka gudanar a sassan kasar ya yi tsammanin adadin zai haura haka, saboda hare-haren da Rasha ke kaiwa ba kakkautawa.

Rahoton dai ya ce, adadin da aka fara kididdigawa ya fara ne tun daga farkon watan da gwamnatin Moscow ta fara mamayar, musamman yadda ta taka rawa a Mariupol, wato inda aka samu adadi mafi girma na  wadanda suka mutu.

Danielle Bell, wanda ke jagorantar tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar, ya ce yakin Rasha a Ukraine dai yanzu haka ya shiga watanni na 21, inda yake ci gaba da lakume rayukan fararen hula.

An danganta mace-macen fararen hular da irin makaman da ake amfani da su wajen kai wa kasar hari, irin su makaman kare dangi ko kuma na roka da sauran su.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma bayyana cewa, karuwar mutuwar mutane da ake samu a cikin watanni ukun da suka gabata ya haura misali, tana mai cewa ya kamata a kawo karshen wannan rikici.

Sama da kaso biyu bisa uku na mutanen da suke mutuwa, shekarunsu sun haura daga 60, kuma masu wadannan shekaru sun kunshi kashi daya bisa hudu na al’ummar kasar.

Sai dai gwamnatin Rasha, ta bayyana karara cewa, hare-harenta da ta ke kaddamarwa a kasar ba kan fararen hula take kaiwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.