Isa ga babban shafi

Zaftarewar kasa ta hallaka sama da mutane 30 a Columbia

Akalla mutane 33 suka mutu, wasu kusan 30 kuma suka jikkata sanadiyar zaftarewar kasa da ta auku a lardin Choco dake yankin arewa maso yammacin kasar Columbia, biyo bayan mamakon ruwan sama mai karfi da aka tafka babu kakkautawa. 

Wasu daga cikin wadanda zaftarewa kasa ta shafa a yankin Choco na kasar Columbia
Wasu daga cikin wadanda zaftarewa kasa ta shafa a yankin Choco na kasar Columbia © Reuters
Talla

Sanarwar da hukumomin kasar suka fitar na cewa faruwar lamarin ya yi sanadiyar rufe biranen Medellín da Quibdo, inda mutane da dama suka nemi mafaka cikin wani gida dake unguwar Carmen de Atrato.

Zaftarewar kasar ta kuma yi sanadiyar tsagewar tituna da dama a wannan yanki, daga bisani motoci suka yi ta ruftawa karkashin kasa, baya ga mutane da ya zuwa yanzu ke cigaba da kasancewa makale a karkashin kasa, kamar yadda magajin garin Choco ya tabbatar. 

Hotunan bidiyo a tashoshin talabijin da shafukan sada zumunta sun nuna yadda tsaunuka suka yi ta rugujewa, da kuma yadda motoci suka yi ta silalewa cikin kasa, dalilin da ya tilasta mutane da dama neman mafaka a wani gida dake kusa unguwar Carmen de Atrato, saidai duk da haka iftila’in ya rutsa da su a wurin, ya kuma yi sanadiyar binne su a cikin kasa.

Kasar Colombia dai na fama da matsalolin fari da sauyin yanayi, abinda ya tilasta kwararrun kasar yin gargadi musamman ga  mazauna yankunan da ake yawan samun saukar ruwan sama, wadanda suka hada kan iyaka kasar da tekun Pacific da kuma dajin Amazon. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.