Isa ga babban shafi

Dukiyar mutane 5 mafiya arziki a duniya ta rubanya tun daga 2020: OXFAM

Wani sabon rahoton kungiyar bayar da agaji ta Oxfam, ya ce daga shekarar 2020 zuwa yanzu, dukiyar da hamshakan attajiran duniya guda biyar suka mallaka ta ninka sau kusan uku, a yayin da kuma mutane biliyan 5 suka kara talaucewa. 

Tambarin kungiyar OXFAM.
Tambarin kungiyar OXFAM. REUTERS/Andres Martinez Casares
Talla

 

Oxfam ta wallafa rahoton ne a yau Litinin, a daidai lokacin da kasashe manyan kasashe da hamshakan attajirai da sauran masu ruwa da tsaki suka hallara a birnin Davos na kasar Switzerland, domin fara taro kan halin da tattalin arzikin duniya ke ciki. 

Kungiyar da ke fafutukar yaki da talauci a duniya ta ce jimillar dukiyar da hamshakan attajiran duniya da suka hada da Elon Musk, da Bernard Arnault, da Jeff Bezos da Larry Ellison da kuma Mark Zuckerberg suka mallaka, ta karu da dala biliyan 464, kwatankwancin karin kashi 114 bisa 100, abinda ya sa a yanzu, su biyar kacal din suka mallaki dala biliyan 869. 

Dangane da matsalar karuwar rata tsakanin masu kumbar ta susa da matalauta kuwa, kungiyar Oxfam ta ce manyan kamfanoni kimanin 148 ne suka samu ribar dala tiriliyan 1 da biliyan 800 daga 2020 zuwa shekarar bara, sai dai kuma a wannan tsakanin kusan mutane biliyan 5 ne, kwatankwacin kashi 60 cikin 100 na yawan al’ummar duniya suka kara talaucewa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.