Isa ga babban shafi

Pakistan ta kai hari da makami mai linzami kan wasu yankunan Iran

Mutane da dama sun mutu yayinda wasu suka jikkata a harin da Pakistan ta kai yankin Sistan-Baluchestan da ke kan iyakar kasar da Iran a matsayi martini kan harin da Tehran ta kai a Talatar da ta gabata.

Mutane 7 harin ya kashe ciki har da kananan yara.
Mutane 7 harin ya kashe ciki har da kananan yara. AFP - SAFIN HAMID
Talla

Akwai dai fargabar tsanantar rikicin a yankin bayan da Iran a baya-bayan nan ke ci gaba da kai hare-hare makwabta a matsayin daukar fansar wadanda ta ce su ke da hannu wajen kalubalantar tsaron kasar.

Ma’aikatar harkokin wajen Pakistan da ke tabbatar da kai harin, ta ce harin ya shafi yankunan da ke matsayin maboyar ‘yan ta’adda a cikin kasar ta Iran.

Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Pakistan ta ce Islambad na mutunta Iran sai dai harin na daren jiya Laraba mataki ne baiwa kanta kariya daga ‘yan ta’addan da ke samun maboya a sassan Iran.

Pakistan wadda ta yiwa hare-haren nata suna da Operation Marg Bar Sarmachar ta ce ta daura aniyar kawar da barazanar da ‘yan ta’addan ke yiwa tsaronta daga Iran.

Iran ta bayyana cewa mutane 7 suka mutu a harin wanda ya kunshi mata 3 da kanan yara 4 da ke zaune a kauyen Saravan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.