Isa ga babban shafi

Blinken ya fara ziyarar mako guda a kasashen Afrika ciki har da Najeriya

Sakataren wajen Amurka Antony Blinken ya fara ziyarar kasashen yammacin Afrika da Sahel wadda ke da nufin bunkasa kawancen kasar da nahiyar musamman yankin Sahel ta fanni tsaro da tabbatuwar demokradiyya.

Ziyarar ta Blinken na zuwa dai dai lokacin da ake samun rarrabuwar kai tsakanin shugabannin Afrika game da yadda Amurkan ke tunkarar yakin Isra'ila a Gaza da kuma na Rasha a Ukraine.
Ziyarar ta Blinken na zuwa dai dai lokacin da ake samun rarrabuwar kai tsakanin shugabannin Afrika game da yadda Amurkan ke tunkarar yakin Isra'ila a Gaza da kuma na Rasha a Ukraine. AFP - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Ziyarar wadda Blinken zai shafe mako guda yana yi zai faro ne da Cape Verde gabanin yada zango a kasashen Ivory Coast da Najeriya da kuma Angola, ziyarar da ke matsayin karon farko cikin watanni 10 da gwamnatin Joe Biden ta shafe a karagar mulki.

Wannan ziyara dai ita ce ta baya-bayan nan da sakataren wajen na Amurka ke kaiwa ketare wadda ba ta shafi yakin Isra’ila a Gaza ko kuma yakin Rasha a Ukraine ba.

Haka zalika ziyarar na zuwa a dai dai lokacin da ake samun rarrabuwar kai tsakanin kasashen Afrika game da yadda Amurka ke tunkarar yakin Isra’ila da Hamas da kuma yakin Rasha da Ukraine.

Ziyarar na matsayin biyan bashi kan alkawarin Joe Biden na ziyartar Afrika cikin shekarar 2023, wanda ake ganin Blinken zai yi amfani da damar wajen karfafa alakar kasar da nahiyar tare da dakushe karsashin China da Rasha a nahiyar.

Ziyara ta karshe da Blinken ya kai Afrika shi ne cikin watan Maris din shekarar 2023 lokacin da ya yada zango a Nijar wanda ya mayar da shi wani babban jami’in Amurka na farko da ya ziyarci kasar ta Sahel da nufin karfafa gwiwa ga shugaba Mohamed Bazoum sai dai kasa da watanni 4 bayan ziyarar Sojoji suka hambarar da gwamnatin ta Bazoum.

Rasha da kamfanin Sojin hayarta na Wagner na ci gaba da kara karfi tsakanin kasashen yankin Sahel musamman wadanda ke fama da matsalolin tsaro dai dai lokacin da Amurka ke ginin sansanin Sojinta a Agadez da ya lakume dala miliyan 100, sansanin da ta ke amfani da shi wajen harba jirage marasa matuki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.