Isa ga babban shafi
YAKIN-GAZA

Kungiyoyin agaji 16 sun bukaci daina ba wa Isra'ila da Falasdinu makamai

Duniya – Kungiyoyin ba da agaji 16 na duniya sun yi kira ga kasashe da su daina ba wa Isra’ila da Falasdinu makamai don kawo karshen yakin da yaki ci, yaki cinyewa tsakanin bangarorin biyu.

Wani hari da Isra'ila ta kai Rafah yau laraba
Wani hari da Isra'ila ta kai Rafah yau laraba REUTERS - STAFF
Talla

A wata sanarwa da suka fitar, kungiyoyin sun shawarci kasashen duniya da su daina ba wa Isra’ila da Falasdinu taimakon makamai domin kawo karshen rikicin Gaza da ke cigaba da haddasa asarar rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba.

Sanarwar ta kara da cewa, hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza na cigaba da haifar da matsalar isar da kayan agaji, yayin da a hannu daya rikicin ke haddasa asarar rayukan fararen hula.

Wasu daga cikin kungiyoyin da suka ratttaba hannu kan wannan sanarwar sun hada da: Amnesty International, Christian Aid, Medecins du Monde da International Network. Sauran kuwa sun hada da Norwegian People's Aid, Oxfam da kuma Save the Children.

Alkaluma na nuni da cewa kashi 95% na makaman da aka tura zuwa Isra’ila sun fito ne daga Amurka kamar dai yadda Martin Butcher, kwararre a batutuwan da suka shafi makamai a kungiyar Oxfam ke cewa, yayin da sauran makaman suka fito daga Jamus, da kuma Birtaniya.

Har ila yau, kungiyoyin sun ce ci gaba da bayar da makamai ga bangarorin da ke da hannu a wannan yaki, zai iya share fage domin zargin su da taimaka wa wajen aikata laifuffukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.