Isa ga babban shafi

An cika shekara guda da girgizar kasar Turkiya da ta kashe mutane dubu 53

Yau ake cika shekara guda da faruwar mummunar girgizar kasar da ta kashe mutanen da yawansu ya haura dubu 53 A Turkiya baya ga wasu kusan dubu 6 a Syria.

Fiye da mako guda aka shafe ana aikin lalubo masu sauran lumfashi a baraguzan gine-ginen na Turkiya da Syria.
Fiye da mako guda aka shafe ana aikin lalubo masu sauran lumfashi a baraguzan gine-ginen na Turkiya da Syria. AP - Ghaith Alsayed
Talla

Yayin taron makokin tunawa da zagayowar ranar, dubban mutane ne suka yi gangami a birnin Antakya mai dogon tarihi rike da alluna masu rubuce-rubucen sake jajantawa ga wadanda ibtila’in ya rutsa da su.

A bangare guda wasu sun rike hotunan wasu da suka rasa rayukansu a ibtila’in na ranar 6 ga watan Fabarairun 2023, da aka bayyana da mafi muni da duniya ta gani a baya-bayan nan.

Da misalin karfe 4 da mintuna 17 na asubahin ranar 6 ga watan ne girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta afkawa sassa 11 na yankin kudu maso gabashin Turkiya da kuma wasu yankuna na Syria da ke iyaka da kasar.

An shafe fiye da makwanni 2 ana aikin laluben mutanen da suka makale a baraguzen gine-gine bayan isar jami'an kai dauki daga kasashe daban-daban.

Wannan ibtila’I dai ya haddasa rabuwar miliyoyin iyalai sa muhallansu wadanda suka koma rayuwa a sansanonin wucin gadi.

A bangare guda hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa ibtila'in girgizar kasar ya tagayyara rayuwar mutane miliyan 23 a kasashen na Turkiya da Syria. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.