Isa ga babban shafi

Rayuwar marigayi Kelvin Kiptum da mutuwarsa ta girgiza duniya

Mutuwar dan wasan da ke rike da kambun gasar gudun fanfalaki na duniya, Kelvin Kiptum sakamakon hatsarin mota, ta girgiza al’ummar duniya da dama.Ko wane ne Kelvin Kiptum?

Marigayi Kelvin Kiptum
Marigayi Kelvin Kiptum REUTERS - ANDREW BOYERS
Talla

An haifi Kelvin Kiptum, ranar 2 ga watan Disambar 1999, a garin Chepsamo da ke kasar Kenya.

Kelvin kasancewarsa dan makiyaya, ya taso yana yi wa iyayensa kiwon shanu, inda yake bin wasu makiyaya zuwa dazukan yankin.

Kiptum ya fara atisayen gudun famfalaki ne a shekarar 2013, lokacin yana dan shekaru 13 da haaihuwa, inda ya halarci gasar gudun fanfalaki na farko, da aka yiwa lakabi da “Family Bank Eldoret Half Marathon” a kasar Kenya, inda ya kare a matsayin na 10.

Motar da marigayin dan wasan tseren fanfalakin ya yi hatsari a cikinta.
Motar da marigayin dan wasan tseren fanfalakin ya yi hatsari a cikinta. REUTERS - STRINGER

Dan-wasan ya fara yin nasararsa ta farko ne a shekarar 2018, daga bisani ya zama zakaran gasar ta duniya da aka yi a Valencia da kuma birnin Landan.

Kazalika ya kafa tarihin lashe gasar da aka yi a Chicago a shekarar da ta gabata inda ya yi nasara a cikin sa‘o’i biyu da dakika 35, wanda har kawo lokacin rasuwarsa shi ke rike da kambun gasar na duniya

Dan wasan na Kenya ya mutu ne tare da kocinsa da yammacin ranar Lahadi a lokacin da suka yi hatsari a motarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.