Isa ga babban shafi
RIKICIN ISRA'ILA DA HAMAS

Ya kamata kasashen kawance su daina taimaka wa Isra'ila da makamai - EU

Kungiyar Tarayyar Turai EU, ta bukaci kasashen da ke kawance da Isra’ila, irin su Amurka, da su dakatar da tura mata da makamai, yayin da ake ci gaba da kashe mutane a Gaza.

Shugaban Diflomasiyyar kungiyar ta EU, Joseph Borrel, lokacin da yake gabatar da jawabi a  wani taron kungiyar da ta gudanar a Faransa.
Shugaban Diflomasiyyar kungiyar ta EU, Joseph Borrel, lokacin da yake gabatar da jawabi a wani taron kungiyar da ta gudanar a Faransa. © AP - Jean-Francois Badias
Talla

Shugaban Diflomasiyyar kungiyar ta EU, Joseph Borrel, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a Brussels, y ace kisan da sojojin Isra’ila ke yi a Gaza ya kai kololuwa.

Ya ce, idan har shugabannin kasashen duniya sun yarda cewa ana kisan da aka ga dama a Gaza, lallai kuwa dole a dakatar da tallafin makaman da ake bawa Isra’ila domin rage kisan da ake yi wa al’ummar Falastinu.

Babban jami’in ya kuma caccaki furucin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da ke cewa akwai bukatar akwai Falastinawa sama da miliyan guda da ke zaman tsira a yankin Rafah.

Yan amai cewa, ina yake son akai wadannan mutane, ko duniyar wata Isra’ila take kokarin mika su ne?.

Yayin da ta sha alwashin share Hamas daga doron kasa, Isra’ila ta kaddamar da manyan-manyan hare-hare a zirin Gaza, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 28,064, yawancinsu mata da kananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.