Sama da mutane biliyan 1 na fama da kiba fiye da kima a duniya
Sama da mutane biliyan daya ne ke fama da matsalar kiba fiye da kima a fadin duniya, inda aka ce adadin ya ninka har sau 4 tun daga shekarar 1990, a cewar wani rahoto da mujallar kiwon lafiya ta Lancet ta fitar.
Wallafawa ranar:
Matsalar ta yi kamari ne a kasashe matalauta, kuma ta yi yawa ne a tsakanin kananan yara da matasa, kamar yadda binciken ya nuna.
Binciken da aka fitar gabanin ranar kiba fiye da kima ta duniya, wanda ke tafe a ranar 4 ga watan Maris, ya yi kiyasin cewa akwai mutane da ke da kiba fiye da kima da adadinsu ya kai miliyan dari 2 da 26 a shekarar `1990, abin da ke nuni da cewa sun karu da ninki 4.
Mujallar ta Lancet ta ce masu binciken sun gwada nauyi da tsayin mutane miliyan 220 a sama da kasashe 164 ne kafin su samu wannan sakamako.
Kwararru sun sha yin kashedi a game da kiba fiye da kima, wadda suka ce yana haddasa cututtuka da dama, wadanda ke kisa farat daya.
Su na kuma bada shawarar a rika motsa jiki a kullayaumin, wanda suka ce yana taimakawa ainun wajen tabbatar da lafiyar jikin dan adam.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu