Isa ga babban shafi

Kwamitin tsaro na MDD zai sake zaman kada kuri'a kan tsagaita wuta a Gaza

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na zaman tattaunawa a yau Juma’a da zai kai ga kada kuri’ar bukatar tilastawa Isra’ila tsagaita wuta a yakin da ta kaddamar kan al’ummar yankin Gaza na Falasdinu.

Wani yanki da Isra'ila ta sake yiwa luguden wuta a Gaza.
Wani yanki da Isra'ila ta sake yiwa luguden wuta a Gaza. AP - Fatima Shbair
Talla

Zaman kwamitin na zuwa a dai dai lokacin da Masar ke karbar bakoncin taron ministocin kasashen larabawa 5 da sakataren wajen Amurka Antony Blinken a kokarin samar da mafitar da za ta kai ga tsagaita wutar dindindin a Gazan.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar akwai kyakkyawan fatan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a wannan karon don kawo karshen yakin da ya tagayyara mutane fiye da miliyan guda da rabi baya ga kashe wasu fiye da dubu 32.

Wannan ce ziyara ta 6 da Blinken ke kaiwa yankin gabas ta tsakiya tun bayan faro yakin na Isra'ila a Gaza da ke masana suka bayyana da mafi munin take hakki da kuma kisa marar kakkautawa da duniya ta gani a shekarun baya-bayan nan.

A baya dai an yi mabanbantan tattaunawa da nufin dakatar da yakin amma ba tare da samun nasarar cimma jituwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.