Isa ga babban shafi

Bayan ragargaza asibitin Al-Shifa, Isra'ila ta janye daga a cikinsa

Sojojin Isra'ila sun janye daga babban asibitin Gaza na Al-Shifa, bayan mamaye shi da suka yi na tsawon makwanni biyu da ya haifar da lalata gine-ginen da ke cikinsa.

Sojojin Isra'ila sun janye daga babban asibitin Gaza na Al-Shifa, bayan mamaye shi da suka yi na tsawon makwanni biyu.
Sojojin Isra'ila sun janye daga babban asibitin Gaza na Al-Shifa, bayan mamaye shi da suka yi na tsawon makwanni biyu. AFP - -
Talla

Isra’ila ta ce ta kai hari asibitin ne ganin yadda mayakan Hamas ke boye a cikinsa, inda ta kashe akalla mayakan kungiyar dari biyu da kuma gano makamai da kudi a cikinsa.

Sai dai Hamas ta karyata zargin da Isra’ila ta yi na cewar, ta na gudanar da aikace-aikacenta ne daga harabar asibitin Al-Shifa da ma sauran asibitocin yankin baki daya.

Ma’aikatar lafiyar yankin Gaza ta ce hare-hare ta jiragen sama da kuma tankokin yaki da Isra’ila ta yi amfani dasu, sun lalata mafi akasarin ginin asibitin.

Wani likita ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa an gano sama da gawarwaki 20 bayan janyewar motocin yakin Isra’ila daga harabar wajen.

An gano gawarwakin mutane da dama wasu daga cikinsu sun rube, a ciki da wajen asibitin Al-Shifa, sannan a yanzu haka asibitin baya aiki.

Sojojin Isra’ila sun kai hare-hare wasu asibitocin yankin Gaza, tun bayan harin da Hamas ta kai cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba bara, lamarin da ya yi sanadiyar lalata asibitoci da dama a yankin Gaza.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, a wani jawabi da ya wallafa shafinsa na X, ya ce wani harin da Isra’ila ta kai kan wasu tantuna da ke tsakiyar asibitin Al-Aqsa, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4.

Sai dai rundunar sojojin Isra’ila ta karyata batun lalata asibitin na Al-Aqsa da aka ce ta yi, inda ta ce ta kai hari ne kawai kan cibiyar gudanar da aikace-aikacen kungiyar Hamas da ke saman ginin asibitin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.