Isa ga babban shafi
YAKIN-GAZA

Isra'ila ta kashe 'yaya da jikokin tsohon Firaministan Falasdinu Ismail Haniya

Duniya – Tsohon Firaministan Falasdinu kuma jigo a kungiyar Hamas, Ismail Haniya ya bayyana cewar Isra’ila ta hallaka ‘yayan sa guda 3 tare da jikokinsa 3 a wani kazamin harin da ta kai musu yau a Gaza.

Ismail Haniya
Ismail Haniya AFP/File
Talla

Haniya ya tabbatar wa kafar yada labaran Al Jazeera da abinda ya kira shahadar ‘yayan na sa tare da jikokinsa sakamakon wannan harin na yau da aka kai sansanin dake kusa da gabar ruwa, lokacin da suke tafiya a cikin mota.

Wannan kisan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ilar taki amincewa da shirin tsagaita wuta domin gudanar da bukukuwan Sallah, yayin da ta kaddamar da wasu munanan hare hare a yau laraba.

Ministan dake kula da yakin dake gudana na Isra’ila, Benny Gantz ya sanar da cewar sun yi nasarar murkushe kungiyar Hamas baki daya, amma duk da haka basu kawo karshen yakin ba, a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar kulla yarjejeniyar zaman lafiya a Alkahira.

Gantz ya yi gargadin cewar sojojin kasar za su kwashe shekaru suna wannan yakin a yankin Gaza wadda kungiyar Hamas ke iko da shi.

Ministan yace a bayyane yake cewa sun yi nasarar murkushe Hamas, da kuma dakile duk wani karsashi da take da shi na kai hari, amma hakan ba zai sa su daina yakin ba.

Yanzu haka Isra’ilar na fuskantar bangarori daban daban a yakin da take gwabzawa, wadanda suka hada da kungiyar Hamas da kungiyar Hezbollah ta Lebanon da wadda ke Syria, yayin da tashin hankali ke ci gaba da gudana a Gabar Yamma da kogin Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.