Isa ga babban shafi

China ta yi kira ga Amurka na gani ta taka muhimmiyar rawa a Gabas ta Tsakiya

Kasar China ta yi kira ga Amurka da ta taka rawar gani a yankin gabas ta tsakiya, kwana guda bayan ganawa tsakanin shugaban diflomasiyyar kasar ta China Wang Yi da takwaransa na Amurka Antony Blinken.

Members of the United Nations Security Council meet on the day of a vote on a Gaza resolution that demands an immediate ceasefire for the month of Ramadan leading to a permanent sustainable ceasefire,
Taron MDD dangane da rikicin Gaza REUTERS - Andrew Kelly
Talla

Mao Ning kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta China ya bayyana cewa da yammacin jiya Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.

Wang Yi ya kuma bayyana rashin jin dadin kasar China kan harin da aka kai kan ofishin jakadancin Iran a kasar Syria, yana mai jaddada cewa, tsaron hukumomin diflomasiyya ba zai iya tauyewa ba, kuma ya kamata a mutunta ikon Iran da Syria.

Israelis rally for the immediate release of the hostages, six months after they were kidnapped during the deadly October 7 attack on Israel by Palestinian Islamist group Hamas from Gaza, near the Knes
Kungiyoyi masu neman a kawo karshen yakin Gaza REUTERS - Ronen Zvulun

Jami’in ya bayyana cewa China za ta ci gaba da taka rawa mai ma'ana a cikin batun yankin gabas ta tsakiya da kuma ba da gudummawa wajen daidaita al'amura, musamman ma bangaren Amurka, ya kamata ta taka rawar gani.

Dangane da batun Isra'ila da Falasdinu, kasar China na yin kira da a tsagaita bude wuta a zirin Gaza a kai a kai domin tabbatar da tsaron fararen hula.

Farraren hula  a yankin Gaza
Farraren hula a yankin Gaza AFP - MOHAMMED ABED

Mao Ning a yau juma’a ya fada: "karuwar tashe-tashen hankula a yankin kan iya haifar da wani sabon rikici da kuma yaduwar zuwa wasu kasashen, kuma ya zama wajibi a kawo karshen rikicin Gaza da wuri-wuri."

Kasar China ta yi kira ga dukkan bangarorin da ke rikici da su aiwatar da kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2728.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.