A cikin shirin mu zagaya Duniya Mahaman Salissou Hamissou ya dubo wasu daga cikin manyan labaren da suka maida hankali zuwa yaki da ta'adanci a yankin Sahel.
Sauran kashi-kashi
-
Cikar shugaban shugaban Najeriya Bola Tinubu shekara guda akan karagar mulki
A cikin shirin Mu Zagaya Duniya akwai cikar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu shekara guda a kan karagar Mulki.sai kuma yadda asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, yayi A wadai da KARUWAR cin zarafi da take hakkin kananan yara a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar a dalilin ta’azzarar ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda. da kuma sauran rahotanni da ke biye dasu.01/06/202420:04 -
Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa
Gwamnan Kano Abba Yusuf ya rattaba hannu a wata doka mai rusa ga baki daya masarautun Kano inda ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa.Bashir Ibrahim Idris dangane da wannan mataki ya tattauna da Abdoulkarim Ibrahim da Nura Ado Suleiman a cikin shirin Duniyar mu a yau daga nan sashen hausa na Rfi.25/05/202420:29 -
Tattaunawa da Dr Kasim Garba Kurfi a shirin Duniyarmu a yau
Wannan shiri na Duniyarmu a yau zai dinga muhawara kan harkokin yau da kullum da ke dauke hankalin jama'a a duk ranar Asabar daga karfe 5.Shirin na wannan mako ya karbi bakucin Dr Kasim Garba Kurfi mai sharhi kuma masanin tattalin arziki.19/05/202420:29 -
Najeriya: Ƙarin albashi da gwamnati ta yi bai burge Ƙungiyar ƙwadago ba
Daga cikin batutuwan da shirin wannan lokaci ya waiwaya akwai, watsin da kungiyar kwadagon Najeriya ta yi da karin albashin ma’aikatan da gwamnatin kasar ta yi.Sai kuma matakin Burkina faso na rufe karin kafafen yada labarai bisa rahoton da suka bayar na kisan fararen hula sama da 200 da sojoji suka yi.A Kenya kuwa Ambaliyar ruwan ce ta lakume rayukan mutane da dama gami da raba wasu kusan dubu 200 da muhallansu.04/05/202419:59 -
Muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata
Masu sauraro daga sashin Hausa na RFI cikin shirin Mu Zagaya Duniya da saba zabo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata, domin bitarsu.A ranar Larabar da ta gabata al'ummar Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da Sallar Idi Karama, wadda aka saba gudanarwa bayan kammala azumin watan Ramadan.13/04/202420:01