Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan Ya Zabi Gwamna Namadi Sambo Mataimakinsa

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya zabi Gwamnan Jihar Kaduna Arch Namadi Sambo, a matsayin mataimakinsa, sakamakon gibin da aka samu, bayan rasuwar shugaba Umaru Musa Yar’adua.Zabin Sambo, wanda yake rike da mukamin Gwamnan Jihar Kaduna, ya kawo karshen cece kucen da ya biyo bayan kokawar neman mukamin, tsakanin Gwamnonin kasar, Yan Majalisu da kuma ma’aikatan Gwamnati dake da alaka da Jam’iyar PDP mai mulki.Ana saran Majalisun kasar, zasu amince da zabin Sambo, kafin rantsar da shi ya kama aiki, a matsayin mataimakin shugaban kasa na uku, a wannan Janhuriyar. 

Arch Namadi Sambo, Gwamnan Jihar Kaduna
Arch Namadi Sambo, Gwamnan Jihar Kaduna RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.