Gbgbo Ya Hana Gwamnan Banki Sauka
Shugaban kasar Cote D'Ivoire Laurent Gbagbo yayi fatali da umarnin kasashen Yammacin Afrika na jiya, dake cewa Gwamnan Babban Bankin Kasar ya sauka daga aiki.Wata sanarwa daga Laurent Gbagbo da aka watsa ta gidan Talabijin na kasar na cewa kada bangaren Alassane Ouattara ya kuskura ya nada sabon Gwamnan Babban Bankin Kasar kamar yadda Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika suka ce yayi.Saboda haka Laurent Gbagbo yace Gwamnan Babban Bankin Kasar Phillip Henry Dakori-Table, kada ma ya tanka ya cigaba da aikin sa.Shugabannin Kasashen yammacin Afrika na bukatar Gwamnan Babban Bankin daya daya sauka ne saboda yadda ya bari Laurent Gbagbo keta barnata dukiyar kasar.
Wallafawa ranar: