Isa ga babban shafi
Britaniya-Libya

Shafin Wikileaks Ya Bankado Wani Sirrin Britaniya

Wasu rahotanni da Jaridar Telegraph da ake bugata a London ta buga, na nuna cewa wani Ministan Britaniya ne ya baiwa kasar Libya shawara yadda za'a yi amfani da ciwon sankara da Maharin jirgin Sama na Lockerbie ke fama da ita domin a sake shi.Bayanan sirri da Shafin yanar giza na Wikileaks ya bayar na cewa Minista Bill Rammell  ne ya rubuta wasika ga takwaran sa na kasar Libya inda yayi bayanin yadda zasu kubutar da Abdelbaset Ali Mohmet al-Megrahi.Alhakin sakin Abdelbaset dai na hannun Hukumomin kasar Scotland, domin jirgin Saman Pan Am 747 wanda aka tarwatsa shi a shekara ta 1988 har ya hallaka mutane 270, a garin Lockerbie na Scotland ya fada. 

Mahari jirgin Sama na Lockerbie Abdelbaset Ali Mohmet al-Megrahi.
Mahari jirgin Sama na Lockerbie Abdelbaset Ali Mohmet al-Megrahi. rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.