Yemen
Ana Ta Zanga Zangan Kyamar Shugaban Yemen
Masu adawa da zanga-zangan gamagari a kasar Yemen sun kara da masu bore,a jere na kwanaki hudu a garin Sanaa, inda mutane akalla hudu suka sami raunuka.Akwai ‘yan jaridu biyu da akayi masu dukan tsiya wajen zanga zangan daya barke a Jamia'r Sanaa inda dalibai ke neman Shugaban kasar daya ajiye mulkin kuma bangaren ‘yan siyasa dake goyon bayan Shugaban kasar.An fara zanga zangan ne da Jamiar aka doshi filin Al-Sabiine kusa da fadar Shugaban kasar Ali Abdallah Saleh.Saidai kuma ‘yan sanda sunyi ta gwabza fada da masu goyon bayan Shugaban kasar dauke da makamai .
Wallafawa ranar: