Isa ga babban shafi
Japan-France

Japan Na Neman Taimakon Faransa Don Farfado Da Nukiliya

Jami'an dake aiki a Ma'aikatar Nukiliya ta tashar Fukushima na kasar Japan sun nemi taimakon kasar Faransa domin farfado da tashar wadda ta lalace.Ministan Masana'antu na kasar Faransa  Eric Besson ya fadi cewa ta hannun ma'aikatar samarda hasken wutan lantarki ta kasar Japan ake neman taimakon.Ministan yace Hukumomi uku na kasar Faransa zasu shiga aikin  kai daukin.Sun hada da Babban Kamfanin Makamashi na EDF, AREVA da kuma Atomic Agency Commission.A makon jiya saida Hukumomin kasar Japan suka nemi jama'a  su  kauracewa harabar ma'aikatar Nukiliyan Fukushima, da nisan akalla kilomita 20 zuwa 30, sakamakon barna da girgizan kasa da mahaukaciyar igiyar ruwan teku suka haifar. 

Wasu Jamian kasar Japan na shirya kai mutane asibiti don aunasu ko sun shaki guba
Wasu Jamian kasar Japan na shirya kai mutane asibiti don aunasu ko sun shaki guba rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.