Isa ga babban shafi
Jamus

Anyi Zanga-Zangan Lumana A Kasar Jamus

Dubban mutane a kasar G Jamus yau suka shiga zanga-zanga domin neman a kawo karshen makaman Nukiliya.Jimillan mutane 144,500 ne suka shiga boren a yankuna 12 dake kasar, inji wadan da suka shirya shi, koda shike ‘yan sanda basu fito fili da alkaluman wadan da suka shiga zanga-zangan ba.Masu zanga-zangan sun tafi har tashan da kasar Jamus ke aikin Nukiliyan ta, da suka hada da Biblis dake kudu maso yammaci da kuma Krummel dake Arewaci.Matakan na biyo bayan mummunan hatsarin da ya auku ne a  tashan Nukiliyan kasar Japan,  da aka samu sakamakon girgizan kasa da igiyar ruwa ta Tsunami.Masu zanga-zangan sun kuma nuna rashin gamsuwar su gameda matakan nuna karfin Soja a Kasar Libya da Afghanistan.  

Angela Merkel Shugaban Gwamnatin kasar Jamus
Angela Merkel Shugaban Gwamnatin kasar Jamus rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.