Libya
'Yan Tawayen Libya Na Neman Goyon Baya
‘Yan Tawayen kasar Libya na chan cikin wani halin rashin sanin abinda suke ciki sakamakon furucin kasashe uku dake cewa basu amince da sabuwar majalisar da suka kafa ba.Da fari mai magana da yawun ‘yan tawayen Jalal al-Gallal ya fadi cewa kasar Canada, Denmark, The Neitherlands da Spain sun amince da sabuwar majalisar ‘yan tawayen kasar ta Libya.Babu bayanai daga Ottawa, amma Ma'aikatun kasashen waje na Copenhagen, the Hague da Madrid sun musanta furucin ‘yan adawan.Ya zuwa wannan lokaci dai kasashen Faransa, Italiya, Qatar da Gambia sun amince da sabuwar majalisar ‘yan tawayen kasar ta Libya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: