Isa ga babban shafi
Egypt

Rikici Tsakanin Musulmi Da Kiristoci Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane 10

Yawan mamata sakamakon fada tsakanin Musulmi da Kiristoci a birnin Alkahira na kasar Masar ya karu zuwa 10, yau lahadi.Jamian tsaron kasar sunce akwai mutane 190 da suka kama suka tsare kuma zaa gurfanar dasu gaban kotun soja.Fira Ministan kasar Essam Sharaf yak ira taron gaggawa na majalisar zartaswan kasar sakamakon wannan fada da mutane akalla 186 suka sami munanan raunuka.An fi gwabza fadan ne a yankin Imbaba dake Arewa maso Yammacin birnin Alkahira, inda wasu musulmi suka nemi kubutar da wata mace da wasu kiristoci suka tsare, saboda tana son shiga addinin musulunci.  

Jami'an tsaro na aikinsu a yankin Imbaba  kusa da Alkahira na kasar Masar
Jami'an tsaro na aikinsu a yankin Imbaba kusa da Alkahira na kasar Masar RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.